Yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare kan garuruwa 3 a Niger, sun fatattaki mutane sama da 1200

Yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare kan garuruwa 3 a Niger, sun fatattaki mutane sama da 1200

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari wasu garuruwa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Niger, inda suka fatattaki mutane sama da 1200 daga gidajensu a yankin.

Sabbin hare-haren na zuwa ne wata guda bayan yan bindiga sun kai hari garuruwa bakwai a wannan yankin, inda suke kashe mata biyu, yaro guda da kuma fatattakar sama dsa mutane 5000 daga gidajensu.

Sabbin hare-haren da aka kai kan garuruwan Gyaramiya, Bataron Jatau da Bataron Waziri ya afku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Laraba.

A cewar wasu shaidu, yan bindigan sun raba mutanen gauruwan da kayayyakinsu ciki harda kayan abinci da fetur.

Sun ce sai dai yan bindigan basu kashe kowa ba, amma sun razana mazauna yankin akan su bar gidajensu zuwa garin Alawa duk a wannan karamar hukumar.

Hakimin garin Alawa, Ibrahim Salihu a wata hirar wayar tarho da Channels TV ya tabbatar da afkuwar lamarin cewa mutane 1200 daga garuruwan uku na samun mafaka a Alawa inda suke neman matsuguni da abinci.

Salihu ya roki gwamnatin jihar da ta kawo masu agaji.

Da yake Magana kan lamarin, kakakin yan sandan jihar, DSP Abubakar Dan-Inna yace yana ta kokarin tuntubar DPO na yankin domin tabbatar da gaskiya, amma bai cimma nasara ba.

KU KARANTA KUMA: Ba lafiya: Yan bindiga sun sake kai hari wata makarantar Kaduna, sun sace shugaban makarantar

DSP Dan-Inna yace a halin yanzu, bai samu rahoto kan harin ba.

Sai dai kuma, yayi saurin karawa da cewa wajen karkara ne sosai sannan kuma cewa samun wayan wajen babban matsala ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel