Rashawa ce ta haddasa mugun talauci a Najeriya - Osinbajo

Rashawa ce ta haddasa mugun talauci a Najeriya - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi babatu na bayyana damuwa a kan yadda talauci ya ke ci gaba da yi wa kasar nan daurin dabai-bayi duk da irin kudaden shiga da ake samu na albarkatun man fetur.

Jaridar Daily Nigerian ta ambato mataimakin shugaban kasar yana cewa, rashawa ce babbar musibar da ta hana arziki ya wadata a kasar duk da kudaden shiga da kasar ta ke samu ta hanyar albarkatun man fetur.

Furucin mataimakin shugaban kasar ya zo ne a ranar Alhamis, yayin halartar taron kaddamar da wata na'urar yaki da rashawa mai amfani da fasahar zamani wadda gidauniyar Akin Fadeyi ta gudanar a birnin Abuja.

A yayin taron wanda Fatima Waziri-Azi ta wakilci mataimakin shugaban kasar, mai ba da shawara ta musamman a kan bin doka da oda ta ofishinsa, ta ce rashawa ce babbar annobar da kara yawan bashin da ke kan kasar nan duk da tulin arziki da kasar ke samu ta hanyar kudaden shiga na albarkatun man fetur.

KARANTA KUMA: Miliyoyin daloli da ake kashe wa akan 'yan gudun hijira ba su da tasiri - Buhari

Dukiyar Najeriya mai tarin yawa ta salwanta a sanadiyar rashawa, inda aka yi sama da fadi da kimanin naira tiriliyan 11 a ma'aikatar makamashi kadai ta kasar tun daga shekarar 1999 kawo wa yanzu.

Ya bayyana damuwa kan koma bayan da rashawa ta haifar a Najeriya, lamarin da ya ce ta fi yin illa ga talakawan kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel