Miliyoyin daloli da ake kashe wa akan 'yan gudun hijira ba su da tasiri - Buhari

Miliyoyin daloli da ake kashe wa akan 'yan gudun hijira ba su da tasiri - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu tasirin da ake gani dangane da ikirarin da kungiyoyin duniya ke yi na batar da miliyoyin daloli a kan 'yan gudun hijira da ke Arewa maso Gabashin kasar nan.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban kasar ya ce babu wani abu da aka gani a kasa duk da irin makudan kudi da kungiyoyin duniya ke kashe wa a kan 'yan gudun hijira da ke Arewa maso Gabas.

Furucin shugaban kasar ya zo ne a ranar Laraba yayin kaddamar da mambobin sabon kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki (ECA) da ya kafa a fadar gwamnatin tarayya, Villa, da ke birnin tarayya, Abuja.

Haka kuma shugaban kasar ya bayyana damuwa ta rashin amince wa da kididdigar da bankin Duniya da kuma Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, suka fitar a kan tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban kasar ya ce sam kididdigar da bangarorin biyu suka fitar a kan tattalin arzikin Najeriya ya sabawa gaskiyar sha'anin da ke wakana a kasar, lamarin da ya ce "mu kenan ba mu da masaniyar abinda ke faruwa a kasar mu".

KARANTA KUMA: Buhari ya ki amince wa da kididdigar bankin Duniya da IMF suka fitar a kan Najeriya

Ya ke cewa, mafi akasarin kididdigar da ake jingina wa kasar Najeriya ta fuskar tattalin arzikinta na zuwa ne a sanadiyar kuskuren hasashe na bankin Duniya, IMF da sauran hukumomi na kasashen ketare, sabanin gaskiyar lamarin da ke kasa.

A Larabar da ta gabata ne asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, cikin babatu da bayyana damuwa, ya ce tsare-tsaren harkokin kudi da gwamnatin Buhari ta shimfida ba za su yi wani tasiri ba wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel