Buhari ya ki amince wa da kididdigar bankin Duniya da IMF suka fitar a kan Najeriya

Buhari ya ki amince wa da kididdigar bankin Duniya da IMF suka fitar a kan Najeriya

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi watsi tare da nuna rashin amincewa da kididdigar da bankin Duniya da kuma Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, suka fitar a kan tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban kasar ya ce sam kididdigar da bangarorin biyu suka fitar a kan tattalin arzikin Najeriya ya sabawa gaskiyar sha'anin da ke wakana a kasar, lamarin da ya ce "mu kenan ba mu da masaniyar abinda ke faruwa a kasar mu".

Furucin shugaban kasar ya zo ne a ranar Laraba yayin kaddamar da mambobin sabon kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki (ECA) da ya kafa a fadar gwamnatin tarayya, Villa, da ke birnin tarayya, Abuja.

Ya ke cewa, mafi akasarin kididdigar da ake jingina wa kasar Najeriya ta fuskar tattalin arzikinta na zuwa ne a sanadiyar kuskuren hasashe da kuma kiyasin bankin Duniya, IMF da sauran hukumomi na kasashen ketare.

Ana iya tuna cewa, a ranar 16 ga watan Satumban da ya gabata shugaban kasa Buhari ya karbi akalar jagorancin majalisar kula da tattalin arziki wanda a mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya rika.

KARANTA KUMA: 'Yan Boko Haram 10 da aka dade ana nema sun shiga hannu

Shugaban kasar ya bayyana damuwa da cewa, kididdigar da ake fitar wa kan tattalin arzikin Najeriya na nufin bamu da masaniyar abin da ke wakana a kasar kenan.

Jerin 'yan majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya da Buhari ya kafa sun hadar da; Farfesa Doyin Salamai, Dr. Muhammad Sagagi, Farfesa Ode Ojuwa, Dr Shehu Yahaya, Dr. Iyabi Masha, Farfesa Chukwuma Soludo, Mr Bismark Rewane da kuma Dr. Muhammad Adaya Salisu.

A baya bayan ne asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, ya ce tsare-tsaren harkokin kudi da gwamnatin Buhari ta shimfida ba za su yi wani tasiri ba wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel