'Yan Boko Haram 10 da aka dade ana nema sun shiga hannu

'Yan Boko Haram 10 da aka dade ana nema sun shiga hannu

- Rundunar sojin kasan Najeriya ta ce ta kama daya daga manyan 'yan ta'addan Boko Haram da ta dade ta nema

- An kama mutumin tare da wasu mayaka 9 na kungiyar Boko Haram

- Hukumar soji ta samu nasarar cafke 'yan ta'addan tare da hadin gwiwar rundunar dakarun tsao na 'ya sa kai

Rundunar dakarun sojin kasan Najeriya ta ce ta samu nasarar cafke wasu 'yan ta'adda na kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a yankin Pulan jihar Borno. Rundunar dakarun sojin ta cafke 'yan ta'addan ne a ranar Laraba, 9 ga watan Oktoba kamar yadda ta bayyana.

Hukumar dakarun sojin ta ce ta samu wannan gagarumar nasara ta cafke 'yan ta'addan tare da hadin gwiwar mambobin dakarun tsaro na 'yan sa kai.

Kalli hoton 'yan ta'addan da hukumar sojin kasan Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook
Kalli hoton 'yan ta'addan da hukumar sojin kasan Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook
Asali: Facebook

Kalli hoton 'yan ta'addan da hukumar sojin kasan Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook
Kalli hoton 'yan ta'addan da hukumar sojin kasan Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook
Asali: Facebook

Daya daga cikin wadanda suka shiga hannu, Alhaji Bukar Modu, mai inkiyar Modu China, ya kasance babban direban mayakan Boko Haram da hukumar sojin kasan ta dade tana fakonsa da kuma nema.

KARANTA KUMA: GITEX: Pantami ya kwadaitar da masu zuba hannu jari a kan ribar da ke Najeriya

Ana iya tuna cewa a Larabar jiya ne hukumar dakarun sojin kasan Najeriya ta bayyana cewa wasu 'yan ta'adda na Boko Haram sun saduda bayan da ta yunwa ta fatattako su daga maboyarsu a sanadiyar tarnaki na yaki da ta'addanci.

Cikin sanarwa da daya daga cikin mai magana da yawun hukumar sojin Kanal Aminu Iliyasu ya fitar, ya bayyana sunayen 'yan ta'addan da suka saduda da suka hadar da Ramat Muhammad, Alhaji Brazil, Bukar Gambo, Waziri Bukar da Bashuna Musa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel