Ba lafiya: Yan bindiga sun sake kai hari wata makarantar Kaduna, sun sace shugaban makarantar

Ba lafiya: Yan bindiga sun sake kai hari wata makarantar Kaduna, sun sace shugaban makarantar

Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare na gwamnati wato 'Government Technical Secondary School' dake kauyen Maraban Kajuru, a karamar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna, inda suka sace shugaban makarantar, Channels TV ta ruwaito.

Harin na zuwa ne mako guda bayan yan bindiga sun sace yan mata shida a makarantar kwaleji na 'Engraver’s college' a kauyen Kakau Daji dake karamar hukumar Chikun a jihar.

Ko da yake, hukumar yan sanda ta jihar bata tabbatar da aukuwar lamarin ba a halin da ake ciki, wata majiya abun dogaro daga gwamnatin jiharta fada ma Channels Television cewa yan bindigan fiye da guda ashirin ne suka shiga makarantar da misalin karfe 12:00 na daren ranar Alhamis, inda suka soma harbe-harbe a iska wanda hakan yayi sanadiyyar razana dalibai da malamai.

KU KARANTA KUMA: Masu gakuwa da mutane na gab da fara bi gida-gida don sace mutane – Majalisa ta koka

Karar bindigogin ne ya tayar da dalibai da malamai daga bacci, inda suka nemi mafaka tare da tserewa daga harabar inda lamarin ke gudana yayin da yan bindigan suka yi garkuwa da shugaban makarantar daga gidansa zuwa inda babu wanda ke da masaniya akai.

Garkuwa da mutane ya zama babban kalubalen da tsaro ke fuskanta a jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel