Hukumar LIRS ta yi sulhu da Jay Jay Okocha a wajen kotu - Inji Lauya

Hukumar LIRS ta yi sulhu da Jay Jay Okocha a wajen kotu - Inji Lauya

A Ranar Larabar nan ne wata Lauya da ke aiki da gwamnatin jihar Legas, Y. A Pitan ta bayyana cewa tsohon ‘dan wasan Super Eagles, Augustine ‘JayJay’ Okocha ya yi sulhu da hukuma.

Hukumar LIRS ta na tuhumar tsohon Kyaftin din Najeriyar ne da laifin kin biyan wasu haraji da ke kansa. Yanzu an yi dace J.J Okocha ya ziyarci ofishin hukumar inda ya biya harajisa a saukake.

Misis Y. A Pitan ta sanar da babban kotun jihar Legas da ke zama a Igbosere cewa babu wasu kudi da hukumar LIRS mai karbar haraji a jihar ta ke bin tsohon mai rike da kambun na Super Eagles yanzu.

Lauyar ta nemi Alkali ya daga zaman shari’ar zuwa wani lokaci domin ta samu damar rubuta sabuwar takardar nema a janye kara. Alkali mai shari’a Adedayo Akintoye ya amince da wannan roko.

Bayan haka kuma Alkali Akintoye ya janye umarnin da aka ba jami’an tsaro a baya na cafke Austin J. J Okocha. A karshe kotu ta dage zama sai zuwa Ranar Alhamis 14 ga Watan Nuwamban 2019.

KU KARANTA: Tsohon Kyaftin din Super Eagles na Najeriya ya rasu

Ana sa rai cewa zuwa lokacin da kotu za ta dawo aiki, wanda ya shigar da kara ya rubuta takardar rokon Alkali ya yi watsi da shari’ar. Hakan na nufin babu wani laifi yanzu a wuyan Tauraron.

A cikin Watan Mayu ne idan ba ku manta ba Lauyoyi su ka bayyana cewa J. J Okocha ya kai ziyara ofishin hukumar LIRS amma ba a iya samun matsaya tsakaninsa da jami’an harajin ba.

Wannan ya sa hukuma ta shigar da kara a Ranar 6 ga Watan Yuni inda ta ke tuhumar tsohon ‘dan kwallon da aikata laifuffuka uku wanda su ka hada kin bayyana kadarorinsa da gujewa haraji.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto kin biyan haraji ya sabawa sashe 56 na dokokin jihar Legas. Bugu da kari wannan ya sabawa sashe na 94 na dokokin haraji da ke cikin kundin tsarin mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel