Masu gakuwa da mutane na gab da fara bi gida-gida don sace mutane – Majalisa ta koka

Masu gakuwa da mutane na gab da fara bi gida-gida don sace mutane – Majalisa ta koka

Majalisar wakilai a ranar Laraba, 9 ga watan Oktoba, ta bukaci dukkanin hukumomin tsaro da su tabbatar sun sa himma wajen nemo dalibai mata shida da ma’aikatan makarantar Engravers College Secondary School, da aka sace a jihar Kaduna.

An bayar da umurnin ne bayan wani jawabi da Hon. Yakubu Bade ya ya gabatar akan lamarin a gaban majalisar wanda kakakinta, Hon Femi Gbajabiamila ya jagoranta.

Majalisa tayi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da shugabannin makarantu masu zaman kansu a fadin kasar da su tsaurara matakan tsaro a cikin harabar makarantun kudi da na gwamnati domin hana kaiwa dalibai kowani irin hari.

A kan haka, majalisar tayi kira ga dukkanin yan Najeriya da su kasance masu lura sosai da tsaro da sanya idanu a kewayen gidajensu sannan suyyi gaggawan jan hankali hukumomin tsaro da zaran sun ga wani zarya da basu aminta dashi ba a kewayensu domin masu garkuwa da mutane na iya fara bin gida-gida domin garkuwa da mutane.

KU KARANTA KUMA: Allah daya gari ban-ban: Kabilar da samari ke kama 'yammata su yi musu dukan tsiya kafin a basu ita su aura

A muhawararsa, Hon Barde yayi bayanin cewa yan bindiga sun sace daliban shida ma’aikata biyu bayan sun samu dammar shiga harabar makarantar kwanan wanda ke a kauyen Kakau Daji a yankin karamar hukumar Chikun hanyar babban tititin Kaduna- Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel