Sanatoci sun fara yunkurin kashe Jam’iyyun siyasar da ba su tabuka komai a zabe

Sanatoci sun fara yunkurin kashe Jam’iyyun siyasar da ba su tabuka komai a zabe

Majalisar dattawan Najeriya tace za ta rage jam’iyyun da za su shiga takara a kasar nan daga 91 da ake da su zuwa kamar biyar. Sanatoci za su kawo kudiri ne a majalisa domin ganin hakan.

A wata ganawa da ‘yan majalisa su ka yi da shugaban hukumar zabe na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu a Ranar Laraba 9 ga Watan Oktoba, Sanatocin sun ce jam’iyyun kasar nan sun yi yawa.

Kamar yadda mu ka ji, Sanatocin sun koka a kan irin tarin jam’iyyu barkatai da za su fitar da ‘yan takara a zaben gwamna da za a yi a cikin kwanaki kadan masu zuwa a jihohin Kogi da Bayelsa.

Da Sanata Ike Ekweremadu yake jawabi a wajen taron, yace ya kamata a soke wasu jam’iyyun. Tsohon shugaban majalisar dattawan yake cewa yawan jam’iyyun Najeriya ya sabawa dokar zabe.

Sanatan na Enugu ta yamma ya bayyana cewa a tsarin dokar zaben Najeriya, duk jam’iyyar da ta gaza cin kujera, ana soke rajistarta ne bayan takara. Yanzu haka akwai jam’iyyu 91 masu rajista.

KU KARANTA: Rigimar shugabanci ta hana APC kafa gwamnati tun bayan zaben 2019

Kabiru Gaya wanda shi ne shugaban kwamitin INEC a majalisar ya yi magana a taron ya ce: “Bai kamata jam’iyyun da su ka gaza tabuka komai a zabe su kuma fitowa a takardar kada kuri’a ba.”

“Dokar zaben da mu ke aiki da ita, ta haramtawa jam’iyyun siyasar da ba su yi abin kirki a zaben da ya gabata sake tsayawa takara ba. Ya kamata mu yi wa dokar zaben garambawul.” Inji Gaya.

Sanatan na Kudancin Kano ya kara da cewa: “Akwai bukatar mu rage jam’iyyun siyasa zuwa mafi akasari biyar. Wannan kwamitin a shirya yake ya yi wannan aiki na rage yawan jam’iyyun nan.”

Sanata Gaya ya na ganin yin wannan zai taimaka wajen rage barnar dukiyar al’umma. A na sa bangaren shugaban INEC ya fadi abin da ya sa hukumar INEC ba ta soke rajistar tarin jam’iyyun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel