Kwara: Rikicin APC ya sa Gwamna ya gagara rantsar da Kwamishoni

Kwara: Rikicin APC ya sa Gwamna ya gagara rantsar da Kwamishoni

Jaridar Daily Trust ta samu labarin abin da ya hana gwamnatin Abdulrahman Abdulrazaq rantsar da Kwamishinonin jihar Kwara bayan tsawon lokaci da karbar mulki daga hannun jam’iyyar PDP.

Bata lokacin da aka samu wajen kafa cikakken gwamnati a Kwara bai rasa nasaba da rikicin da ya shigo cikin jam’iyyar APC. Rikicin dai har ta kai an fara samun matsala a tafiyar gwamnatin jihar.

An samu baraka ne a jam’iyyar APC mai mulki inda wata kungiyar Taware mai suna Kwara APC Unity Group ta fito. Charles Olufemi Folayan da Shehu Bashir ne ke jan ragamar wannan kungiyar.

Olufemi Folayan shi ne ke rike da kujerar shugaban a kungiyar KAUG na ‘Yan Taware, yayin da Shehu Bashir ya ke matsayin Sakatatarensa. A wani jawabi, KAUG sun tabbatar da samun sabani a APC.

KU KARANTA: Buhari ya gana da wadanda su ka yi masa Minista a 1985

Shugaban APC na jihar Kwara, Bashir O. Bolarinwa, ya koka da yadda abubuwa su ke tafiya a cikin jam’iyyar inda ya zargi wasu tsirarru da son kai a maimakon a ceci al’ummar jihar ta Kwara.

Gwamna Abdulrazaq ya musanya cewa akwai rabuwar kai a cikin gidan jam’iyyar APC inda ya yi wa mutane alkawarin cewa zai kafa gwamnati mai karfi da zarar ya gama wasu tattaunawa.

Daga cikin wadanda gwamnan ya zaba a matsayin Kwamishinoninsa akwai Sa’adatu Modibbo-Kawu; Arinola Fatimoh Lawal; Aisha Ahman Pategi, da Joana Nnazua Kolo mai shekara 26.

A Ranar 9 ga Watan Okotoba ne kuma aka sake aika sunayen mutum 6 a majalisa. Salman Jawondo, Aliyu Sabi, Dr Rabiu Rasaq, Aliyu Muhammed, Wahab Agbaje Muritala Olarewaju.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel