Rundunar sojin Najeriya ta cafke babban direban Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta cafke babban direban Boko Haram

- Rundunar sojin Najeriya, ta ce ta kama jiga-jigan mayakan 'yan ta'addan Boko Haram harsu 10

- Ta bayyana cewa, ta cafke harda babban direban kungiyar Boko Haram din

- Ba a nan suka tsaya ba, sun ceto fararen hula 12 da suka hada da mata da kananan yara da kungiyar ke garkuwa dasu

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa, ta cafke jiga-jigan mayakan 'yan ta'addan Boko Haram harsu 10 a jihar Barno.

A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na tuwita, ta ce cikin 'yan ta'addan da ta cafke, harda babban direban kungiyar, Alhaji Bukar Modu, wanda aka fi sani da Modu China.

Rundunar ta bayyana cewa, Modu China shi ne lamba ta 89 a cikin jerin sunayen 'yan ta'addan Boko Haram da rundunar ke nema ido rufe.

KU KARANTA: Kotu ta yankewa wata budurwa shekaru 10 a gidan gyaran hali akan kisan kai

Rundunar ta ce ta kama 'yan ta'addan ne a samamen da ta kai ranar Talata, 9 ga watan Oktoba a dajin Pulka da ke jihar Barno.

A wani cigaba kuma da aka samu a ranar Litinin duk dai cikin wannan makon, rundunar tace ta kama wasu mutane 8 da take zargin 'yan ta'addan Boko Haram din ne a samamen da ta kaddamar don kakkabe 'yan ta'addan a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu zuwa Bama.

Ta ce ta ceto mutane 12 da suka hada da mata da kananan yara da 'yan ta'addan ke garkuwa dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel