Jami'ar jihar Legas ta kafa kwamitin bincike akan malamai masu lalata da dalibai

Jami'ar jihar Legas ta kafa kwamitin bincike akan malamai masu lalata da dalibai

- Biyo bayan zargin da ake wa malaman jami'ar har biyu akan lalata da dalibai, jami'ar jihar Legas ta kafa kwamitin bincike akan lamarin

- Jami'ar ta bukaci dalibai da malaman jami'ar masu karin bayani akan lamarin da su garzaya don badawa

- Hukumar jami'ar ta tabbatarwa dalibai, malamai, tsoffin dalibai da iyaye, cewa za a yi hukunci yadda yakamata

Biyo bayan zargin da ake wa malamai biyu na jami'ar jihar Legas akan lalata da dalibai mata, hukumar jami'ar ta hada kwamiti don binciken lamarin.

Boniface Igbeneghu, babban malami, da Samuel Oladipo, malami a fannin tattalin arziki na jami'ar, an bankado asirinsu ne bayan da BBC ta saki faifan bincikenta mai suna 'Idon Afirka'.

KU KARANTA: Kotu ta yankewa wata budurwa shekaru 10 a gidan gyaran hali akan kisan kai

Taiwo Oloyede, mataimakin shugaban sadarwa na jami'ar jihar Legas, ya bayyana cewa, a ranar Laraba 9 ga watan Oktoba, an nada kwamiti wanda farfesa Ayodele Atsenuwa ke jagoranta, shugaban fannin karatun shari'a na makarantar.

Ya kuma tabbatar da cewa, jami'ar ta dakatar da malaman daga aiki.

Yace za a yi abin cikin adalci kuma za a yi hukunci yadda yakamata.

Jami'ar ta kara da baiwa dalibai da malamai damar bayyana duk wata shaida da ta shafi lamarin matukar sun santa. An kara da tabbatar musu da cewa, akwai matakan tsaro da jami'ar zata dauka don tabbatar da tsaronsu.

Takardar itace kamar haka: "Kwamitin zai binciki zargin cin zarafin da ake wa Dr. Boniface Igbeneghu da Dr. Samuel Oladipo,"

"Kamar yadda kafar yada labarai ta jami'ar ta sanar a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, 2019, an ga Dr. Samuel a faifan binciken BBC. A dalilin hakan ne aka dakatar dashi a take tare da haramta masa shigowa yankin karatu na jami'ar har zuwa lokacin da za a kammala bincike."

Ta kara da cewa, "Dalibai da malamai da ke da bayani da ya shafi hakan ana bukatar da su bayyana. Akwai tabbacin kariyarsu. Muna tabbatarwa dalibai, malamai, tsoffin dalibai da iyaye cewa za a shawo kan wannan matsalar da gaggawa. Kuma za a yi hukunci yadda ya dace."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel