Tattalin arziki: Najeriya, Afrika ta Kudu da Angola sun gaza a 2019 - Bankin Duniya

Tattalin arziki: Najeriya, Afrika ta Kudu da Angola sun gaza a 2019 - Bankin Duniya

Babban bankin Duniya ya koka da tsarin da ake bi wajen fitowa daga cikin matsin tattalin arzikin da aka shiga ciki a kasashen Afrika da su ka hada da Najeriya da kasar Afrika ta Kudu da Angola.

Kamar yadda mu ka samu labari Ranar Laraba, 9 ga Oktoba 2019, bankin na Duniyan ya na ganin cewa tattalin arzikin wadannan kasashe ya na yin tafiyar hawainiya yayin da wasu ke ganin cigaba.

Bankin ya bayyana wannan ne a wani zama da ya yi a Birnin Washington a kasar Amurka domin duba halin da tattalin arzikin kasashen Afrika su ke ciki. A kan yi wannan zama ne sau biyu a shekara.

A cewar bankin, tattalin arzikin wadannan kasashe ba ya motsawa yadda ya kamata duk da tsare-tsaren da aka kawo. Halin da kasuwannin Duniya su ka shiga ya kara taimakawa wannan matsala.

KU KARANTA: Kwastam sun yi kasuwa bayan sun samu Biliyan 5 a filin jirgin Legas

A rahoton da aka fitar, an bayyana cewa babu wani cigaban kirki da aka samu a bangaren da ke wajen man fetur a Najeriya. A Afrika ta Kudu kuwa masu zuba hannun jari ne ke tserewa a kasar.

A daidai wannan lokaci bangaren fetur ya na ta wala-wala a kasar Angola. Bankin na Duniyan yake cewa tattalin arzikin mafi yawan kasashen Nahiyar zai cigaba da habaka illa ukun nan.

Wani babban jami’in babban bankin na Duniya kuma mataimakin shugaban bankin na yankin Afrika, Mista Hafez Ghanem, yace hanyar da za a taimakawa Afrika shi ne ta karfafawa matansu.

Daga cikin yadda za a iya ba mata karfi kamar yadda aka zayyana akwai hanyar; koya masu aiki, ba su jari cikin sauki tare da ba su damar mallakar filaye, sama masu aiki da renon masu tasowa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel