Lakcaran da aka kora a ABU akan lalata da dalibai ya samu sabon aiki a jami'ar KASU dake Kaduna

Lakcaran da aka kora a ABU akan lalata da dalibai ya samu sabon aiki a jami'ar KASU dake Kaduna

- Jami'ar jihar Kaduna KASU ta dauki wani Malamin jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria da aka kora daga aiki

- Mutumin dai an kore shi daga ABU ne saboda an gano cewa yana lalata da dalibai mata sannan ya ba su makin jarrabawa

- Yanzu haka dai Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya ce zai dauki mataki akan wannan lamari

Wata mai amfani da shafin sadarwa na Twitter mai suna @ms_jolena ta wallafa wani labari a shafinta inda take bayyana yadda wani Malamin jami'ar Ahmadu Bello University (ABU) mai suna A.B Umar, wanda aka kora saboda yana neman dalibai da lalata an sake daukar shi aiki a wata jami'ar.

A cewar @ms_jolena, malamin yanzu jami'ar jihar Kaduna (KASU) ce ta dauke shi aiki, kimanin kilomita 70 daga jami'ar ABU din da aka kore shi.

Matar ta wallafa rahoton kamar haka: "ABU ta kori A.B Umar saboda neman dalibai da yake yi da lalata, yanzu haka wata jami'ar da nisan su bai wuce kilomita 70 ba ta sake daukar shi aiki domin ya cigaba da kwanciya da ba ta yaran mutane.

KU KARANTA: Rikita-rikita: Amarya ta haihu wata hudu kacal da yin aure a Kano

"Daga yaya zaku dauki mutum irin wannan aiki bayan kun riga kun san halinsa ba mai kyau ba ne. Jami'ar jihar Kaduna ce ta dauke shi aiki."

Da yake mayar da martani akan wannan rubutu da matar tayi, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce kwamishinan ilimi da alkalin alkalai na jihar Kaduna za su fara bincike akan wannan lamari kuma za a dauki mataki akan wannan lamari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel