Da duminsa: Yanzun nan wata tsohuwar Minista ta kashe kanta

Da duminsa: Yanzun nan wata tsohuwar Minista ta kashe kanta

- Bayan shafe shekaru masu yawan gaske tana fama da matsalar bakin ciki da bacin rai a rayuwar ta

- A karshe Ministar ta yanke hukuncin daukar ranta a lokacin da take da shekaru 69 a duniya

- Ministar mai suna Ella Vogelaar ta kashe kanta a jiya Laraba 9 ga watan Oktobar nan

Iyalan wata tsohuwar minista ta kasar Dutch mai suna Ella Vogelaar ta kashe kanta a jiya Laraba 9 ga watan Oktobar shekarar 2019, ta kashe kanta tana da shekaru 69.

Iyalan na ta sun bayyana cewa Vogelaar tana fama da tsananin bacin rai da bakin ciki na tsawon lokaci, inda a karshe ta yanke hukuncin daukar ranta.

Vogelaar dai ita ce shugabar wani babban kamfani a kasar Dutch mai suna Oxfam Novib, inda ta jagoranci kamfanin daga shekarar 2004 zuwa shekarar 2007, jaridar Xinhua ta ruwaito.

KU KARANTA: Dawafi 7x7 muka yiwa Ganduje kafin mu samu ya cire jar hular dake kan shi saboda kulle-kullen dake cikinta - Ali Baba

Daga watan Fabrairun shekarar 2007 zuwa 2008 ta rike mukamin Ministar gidaje a gwamnatin Firaministan kasar Jan Peter Balkenende.

Ta bar wannan mukamin nata watanni hudu da samu, inda ta bar jam'iyyar da take ta koma wata.

A lokacin da take Minista, Vogelaar ta kawo wasu tsare tsare masu muhimmanci a biranen kasar, inda kuma aka yi alfahari da sauyin da ta kawowa kasar a wannan dan kankanen lokaci da ta rike mukamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel