Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Mataimakin gwamnan jihar Legas, Obafem Hamzat a ranar Laraba 9 ga watan Oktoba ya kama wasu direbobi wadanda ke saba dokokin tuki a Carter bridge da Mile 2 a birnin Legas.

Hamzat yana kan hanyarsa ta zuwa Jami'ar jihar Legas (LASU) inda zai bayar da lakca ne amma ransa ya baci saboda yadda ya ga direbobi suna ta saba dokokin tuki hakan yasa ya sauka da kansa domin ya kama masu karya doka.

Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)
Mataimakin gwamnan Legas, Femi Hamzat tare da wani direban danfo da ya kama yana 'aron hannu'
Asali: Twitter

Ya mika su ga jami'an hukumar kula da cinkoson ababen hawa na jihar, LASTMA domin a hukunta su kamar yadda Linda Ikeji Blog ya wallafa.

Ga sauran hotunan a kasa:

Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)
Mataimakin gwamna Legas ya tsare wani direba da ya yi 'aron hannu'
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rigingimu: Mambobin PDP sun fice daga zauren majalisar dokokin jihar Filato

Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)
Mataimakin gwamna jihar Legas yayin da ya ke magana da wani direba ya yi 'aron hannu'
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel