Zaben Kogi: Jigo a APC, Halima Alfa ta marawa Gwamna Bello baya

Zaben Kogi: Jigo a APC, Halima Alfa ta marawa Gwamna Bello baya

- Magoya bayan Gwamna Yahaya Bello suna ta karuwa

- A baya-bayan nan ne Hajiya Halima Alfa ta ce gwamnan mai ci na Kogi za ta mara wa baya

- Alfa fitacciyar 'yar siyasa ce mai al'umma sosai musamman a karkara a mazabar Kogi ta Gabas

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu goyon bayan wata jigo a siyasar jihar gabanin zabewn gwamna da za a gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Hajiya Halima Alfa, jigo a jam'iyyar APC kuma shugaban mata ta shiga jerin wadanda suke goyon bayan takarar gwamnan a karo na biyu.

Hajiya Alfa dai fitacciyar 'yar siyasa ce mai jama'a musamman a kauyuka a mazabar Kogi ta Gabas na jihar.

DUBA WANNAN: Rigingimu: Mambobin PDP sun fice daga zauren majalisar dokokin jihar Filato

Fitacciyar 'yar siyasan ta bayyana hakan ne yayin ziyarar da ta kai wa gwamnan a gidansa da ke Abuja a ranar 8 ga watan Oktoba.

Ta ce ta yanke shawarar goyon bayan Gwamna Bello ne saboda magoya bayanta da abokan shawarar ta na siyasa duk sunyi ammana da shi.

Tsohuwar 'yar takarar gwamnan a karkashin jam'iyyar APC ta ce gwamna Bello ya taka rawar gani sosai duk da rashin kudi da ake fama da shi a kasa da shari'a da ya yi tayi a kotu.

Ta kuma yabawa gwamnan saboda hadin kan 'yan jihar da ya yi daga addinai daban-daban da kabilu wadda hakan ya kara inganta tsaro a jihar.

Ta shawarci 'yan kabilar Igala su rungumi cigaba suyi watsi da duk wata manufa da ba za ta kawo cigaba da hadin kai ba da wasu tsirarun 'yan siyasa a jihar ke da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel