Kisan farar hula: Saudiyya ta yi Alla-wadai da harin da Turkiyya ta kai kasar Syria

Kisan farar hula: Saudiyya ta yi Alla-wadai da harin da Turkiyya ta kai kasar Syria

Kasar Saudiyya ta yi Alla-wadai da mummunan harin da dakarun sojin kasar Turkiyya suka kai a kan Kurdish da ke arewa maso gabashin kasar Syria tare da bayyana hakan da cewa zai kawo koma baya a yakin da ake yi da 'yan ta'adda a yankin.

"Harin da dakarun sojin kasar Turkiyya suka kai zai kawo a nakasu a tsaron yankin da kuma kara lalata daidaiton da ya fara dawowa yankin," a cewar ma'aikatar harkokin waje ta kasar Saudiyya, a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Laraba.

Sakon ya cigaba da cewa, "kai harin zai kawo nakasu a kokarin da kasashen duniya ke yi na kawo karshen aiyukan kungiyar IS mai cibiya a yankin," kamar yadda kamfani dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce kasar Turkiyya ta yi raguwar dabara da ta kai hari kasar Syria.

Shugaba Trump ne ya janye sojojin kasar Amurka daga yankin, wani lamari da wasu suka fassara da tamkar bayar da dama ga kasar Turkiyya domin ta mamaye yankin.

A ranar Laraba ne dakarun sojin sama na kasar Turkiyya suka yi luguden wuta a yankin arew maso gabashin kasar Syria na Kurdish.

Harin ya yi sanadiyar mutane 15 wadanda 8 daga cikinsu an tabbatar da cewa farar hula ne, marasa makamai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel