Badakkalar naira miliyan 12: EFCC ta kama ma’ajin wata masarauta daga jihar arewa

Badakkalar naira miliyan 12: EFCC ta kama ma’ajin wata masarauta daga jihar arewa

Hukumar yaki da cin-hanci da kuma hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da Mansur Mahmoud, ma’ajin masarautar Ringim dake jihar Jigawa sakamakon zarginsa da aikata laifin cin-hancin kudi naira miliyan 12.430.

Hukumar ta shigar da karar ne a babbar kotun jihar dake garin Hadejia inda Alkali, Jastis Ado Kudu ke gudanar da shari’ar.

KU KARANTA:Najeriya ba ta bukutar Majalisar dattawa, inji wani Gwamnan APC

Mansur ya karbi kudin ne a matsayin bashi daga hannun wani mutum inda ya ce zai biya ma’aikatan masarautarsa albashi, kana kuma zai biya bashin ba da jimawa ba. Amma kuma bayan ya karbi kudin sai yayi mirsisi ya ki biya.

Mai magana da ywaun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce wanda ake zargin ya ki amincewa da laifinsa. Wilson ya fadi wannan maganar ne ranar Laraba 9 ga watan Oktoba a Abuja.

Lauyan EFCC wanda shi ne ya shigar da karar ya roki kotu da ta aika da Mansur zuwa gidan kaso kafin ranar da za a dawo domin cigaba da shari’a.

Jastis Kudu ya bayar da belin Mansur a kan naira miliyan 10. A karshe kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Oktoba.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta kashe majalisar dattawa domin a cigaba da amfani da majalisa guda daya kacal wadda ita ce majalisar wakilai.

Gwamnan ya fadi wannan maganar ne a wurin taron tattalin arzikin Najeriya karo na 25 wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

https://punchng.com/efcc-arraigns-ringim-emirate-accountant-for-n12m-scam/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel