EFCC ta samu umurnin kotu na tsare Maina a hannunta

EFCC ta samu umurnin kotu na tsare Maina a hannunta

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta samu wani umurni na babbar kotun birnin tarayya, Bwari, domin tsare tsohon Shugaban hukumar fansho, Mista Abdulrasheed Maina da dansa Faisal, a hannunta har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake cigaba da yi.

An bayar da umurnin ne a ranar 7 ga watan Oktoba, 2019 biyo bayan wani bukata da hukumar yaki da rashawar ta gabatar a kotu, kan ta baiwa hukumar ikon tsare wanda ake karan a hannunta na tsawon kwanaki 14.

Sai dai kotun ta bayyana cewa ana iya sake duba umurnin idan bukatar hakan ya taso, hukumar ta bayyana a wani jawabi.

Rundunar tsaro na DSS ce ta kama Maina da dansa a wani otel a Abuja biyo bayan taimakon da hukumar ta nema daga wajenta.

Sannan aka mika su ga EFCC domin cigaba da bincike da hukuntasu akan zargin sama da fadi akan wasu kudade.

KU KARANTA KUMA: Gwamna AbdulRazaq ya sake aike wa da sunayen wasu kwamishinoni 6 majalisar dokokin jihar Kwara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar yaki da cin hanci da ashawa (EFCC) ta cika takardun kotu domin kwace wasu adadin kadarori da aka gano suna da nasaba da tsohon Shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina.

Hakazalika, hukuma yaki da rashawar ta cika wani takarda domin samun umurnin tsare tsohon mataimakin daraktan na hukumar ta CIPPO, wanda a makon da ya gabata ne hukumar tsaro na sirri DSS suka mika shi ga EFCC bayan sun kama shi a wani otel a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel