Shugaba Buhari na shan caccaka akan kara wa’adin aikin mai tsaronsa da shekara 4

Shugaba Buhari na shan caccaka akan kara wa’adin aikin mai tsaronsa da shekara 4

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na fuskantar suka akan tsawaita shekarun aikin babban mai tsaronsa, Abdulkarim Dauda, na tsawon shekara hudu, wani yunkuri da masu suka suka bayyana a matsayin wanda baya bisa ka’ida sannan cewa rage ikon hukumar yan sanda ne.

An tattaro ceewa sau biyu aka kara wa Dauda, matsayi cikin shekaru uku sakamakon matsayinsa na hadimin Shugaban kasa.

Doka ta bayyana cewa dan sanda na iya cigaba da kasancewa a aiki na tsawon shekara 35 ko kuma har sai ya cika shekara 60 a duniya ko kuma wanda ya fara zuwa farko.

Sai dai a wani takarda da ya billo dauke dxa sa hannun sakataren rundunar yan sandan Najeriya, AIG Usman Alkali, dauke da lamba DTO:041500/10/2019, an bayyana cewa za a bar Dauda, wanda ya kasance kwamishinan yan sanda ya cigaba da kasancewa a aiki har zuwa 2023.

Hakan na nufin cewa Dauda zai shafe shekara 39 a aiki a lokacin da za a yi masa ritaya, alfarma da Inspekta Janar na yan sanda ne kan ci moriyarsa.

Wasikar, wanda ya karade shafukan zumunta a ranar Laraba, ya sha suka daga wasu yan Najeriya wadanda suka ce Shugaban kasar bai bin tsari da dokar aiki.

Wani shahararren mai sukar gwamnati, Farfesa Farooq Kperogi, yayi zargin cewa dan sanda dan uwan Shugaban kasar ne don haka ne yake samun karin girma akai-akai.

KU KARANTA KUMA: Abinda Buhari ya fada yayin ganawarsa da tsofin ministocinsa

Jagoran tsarin aikin yan sanda na kasa, Okey Nwanguma, ya bayyana matakin Shugaban kasa a matsayin wanda baya bisa ka’ida.

Nwanguma yace hukumar yan sanda ce kadai keda ikon karawa jami’in dan sanda wanda ba IG ba aiki ba wai Shugaban kasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel