Najeriya ba ta bukutar Majalisar dattawa, inji wani Gwamnan APC

Najeriya ba ta bukutar Majalisar dattawa, inji wani Gwamnan APC

Gwaman jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce Najeriya za ta iya soke majalisar dattawa saboda kasar za ta iya dogara da majalisa guda daya kacal wato majalisar wakilai.

Gwamnan yayi wannan furucin ne a wurin taro na musamman game da tattalin arzikin Najeriya karo na 25 wanda aka gudanar a Abuja.

KU KARANTA:Mugabe: Iyalan marigayin na shirin mayar da kabarinsa gidan tarihi – Rahoto

Fayemi ya ce: “Akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta duba fadinta, ni ina goyon bayan tsarin majalisa guda daya kacal wadda ita ce majalisar wakilai saboda su ke wakiltarmu.”

“Jihar Ekiti na da sanatoci uku haka ita ma jihar Legas sanatoci uku ne da ita duk da kuwa bambancin girman jihohin. A ganina babu adalci cikin lamarin, zai fi kyau idan gwamnati ta soke majalisar dattawan gaba daya. Saboda akwai abubuwa masu muhimmanci da yawa da gwamnatin za ta iya yi.” Inji Fayemi.

Idan baku manta ba dai majalisar dattawa na dauke ne da sanatoci 109 yayin da majalisar wakilai ke cike da mambobi 360 daga jihohin Najeriya 36.

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, Majalisar dattawa ta soma tafka muhawara a kan kasafin kudin 2020 a ranar Laraba 9 ga watan Oktoba, 2019.

Majalisar na kokarin kammala bita tare da tantance kasafin kudin kafin watan Disemban wannan shekarar. Shugaba Buhari ne ya gabatarwa gamayyar majalisar dokokin Najeriya kasafin tiriliyan N10.33 a ranar Talata 8 ga watan Oktoba.

https://www.thecable.ng/fayemi-we-can-do-away-with-senate

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel