El-Rufai ya dauki mataki nan take bayan an sanar da shi cewa Jami'ar Kaduna ta dauki malamin da aka kora saboda lalata da mata aiki

El-Rufai ya dauki mataki nan take bayan an sanar da shi cewa Jami'ar Kaduna ta dauki malamin da aka kora saboda lalata da mata aiki

- Wata mai shafi a tuwita ta wallafa wani zargi da ake na cewa jami'ar jihar Kaduna ta daukesa aiki

- Hakan kuwa ya ja hankalin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru ElRufai

- Babu jimawa ya maida martanin cewa yayi umarni ga kwamishinan ilimi da babban lauyan jihar da su binciki zargin

Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya bada umarnin binciken abinda ya gani a shafin tuwitar wata.

Gwamnan yaga budurwar ne ma bayanin yadda jami'ar jihar Kaduna ta kara dauki malamin da jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ta kora akan lalata da dalibai mata aiki.

Gwamnan jihar Kaduna ya bukaci a bincika gaskiyar lamarin ta hanyar bincikar hukumar jami'ar jihar Kaduna.

Mai shafin tuwitan ta wallafa hakan ne bayan fitar faifan bidiyon binciken BBC akan malamai masu lalata da dalibai mata don maki.

KU KARANTA: Tsananin yunwa ta sanya 'yan ta'addan Boko Haram mika kansu ga rundunar sojin Najeriya

Yayin maida martani ga zargin, gwamnan ya nuna matukar razanarsa akan zancen. Don haka ne ya tabbatar da cewa zai yi kira ga kwamishinan ilimi tare da babban lauyan jihar don bincikar lamarin.

"Na matukar razana da jin wannan zancen. Zanyi umarni ga kwamishinan ilimi da babban lauyan jihar Kaduna da su gaggauta bincikar zargin nan. Muna godiya da kika jawo hankalinmu akan hakan." A yadda gwamnan ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Idan bazamu manta ba, a kwanakin bayane jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ta kori wasu malamanta daga aiki akan zarginsu da take da lalata da dalibai mata.

Kwatsam kuma sai ga faifan bidiyon binciken sirri da wata 'yar jarida mai aiki da BBC, Kiki Mordi, tayi.

Ganin hakan ne jama'a suka farga cewa wannan matsala ta neman dalibai mata da malaman jami'a ke yi fa ta zamo ruwan dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel