Wata sabuwa: A yanzu mata na iya shiga aikin soja a kasar Saudiyya

Wata sabuwa: A yanzu mata na iya shiga aikin soja a kasar Saudiyya

Kasar Saudiyya ta sanar a ranar Laraba cewa za ta bari mata a masarautar su fara aiki a rundunar soji yayinda take shirin yin garambawul a tattalin arziki da zamantakewar kasar.

Wannan yunkurin shine mataki na baya-bayan nan a kokarinta na kara wa mata a masarautar yanci, duk da cewa kungiyoyin kare hakki na zargin Riyadh da ragargaza akan mata masu raijin kwato yanci.

“Wani mataki na tallafawa,” ministan harkokin waje ya wallafa a shafin Twitter, inda ya kaa da cewa mata za su samu damar aiki a matsayin kofur ko sajen.

A bara, kasar Saudiyya ta umurci mata da su shiga aikin hukumomin tsaronsu.

Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, ya amince da yin sauye-sauye bisa kudirin ba mata yanci, ciki harda barinsu su tuka mota da kuma tafiya kasar waje ba tare da neman yarda daga waliyi namiji ba.

KU KARANTA KUMA: Yadda na kashe wata babbar kwamandar sojin ruwa – Mai laifi

Amma a lokaci guda ya yi na’am da kama masu raijin kare hakkin mata da dama, ciki harda Loujain al-Hathloul.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel