Sabuwar doka: Za a iya daure ki na tsawon shekaru biyu a kan hana miji hakkin kwanciya - 'Yan sanda sun gargadi matan aure

Sabuwar doka: Za a iya daure ki na tsawon shekaru biyu a kan hana miji hakkin kwanciya - 'Yan sanda sun gargadi matan aure

Za a fara cajin matan aure da laifin tauye hakkin mazansu wanda yin hakan zai iya jawo musu hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ko kuma biyan tarar kudin kasar Ghana GHc6,000 ko kuma duk biyun idan har laifin ya tabbata a kansu.

Da yake sanar da sabuwar dokar, Mista George Appiah-Sakyi, shugaban sashen kula da rigingimun cikin gida a hukumar 'yan sanda (DOVVSU) a kasar Ghana, ya ce maza kan iya shigar da korafin matansu domin a ladabtar da su da sabuwar dokar.

A cewarsa, doka ba iya kan mata ta tsaya ba, za ta hada har da mazan da ke hana matansu hakkinsu na kwanciya. Kazalika, ya ce su ma matan da mazansu ke hana su hakkinsu na aure zasu iya shigar da korafinsu a ofishin rundunar 'yan sanda.

Da yake gabatar da jawabi a wurin wani taron shugabannin addini da birnin Cape Coast, babban jami'in dan sandan ya ce doka ta tanadi hukunci a cikin kundin hukunta laifuka na shekarar 2007 ga duk wanda aka samu da laifin muzguna wa abokin zamansa na aure.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada wa mambobin kwamitin ECA a ganawarsu ta farko

"Idan mazanku basa cin abincin da kuka girka musu ko kuma basa saka ku farin ciki ko suka ci mutuncinku, za ku iya kawo kararsu. Idan mijinki yana dawowa gida da tsakar dare kuma baku son hakan, za ku iya kawo kararsa sashen DOVSSU.

"Idan matarka na kwanciya na matsatsen wando don kar ka kusance ta da daddare, ka kawo mana rahoto a DOVVSU," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel