Mugabe: Iyalan marigayin na shirin mayar da kabarinsa gidan tarihi – Rahoto

Mugabe: Iyalan marigayin na shirin mayar da kabarinsa gidan tarihi – Rahoto

-Kabarin marigayi Robert Mugabe zai zama gidan tarihi a Zvimba

-Leo Mugabe mai magana da yawun bakin iyalan Mugabe ne ya fitar da wannan labarin

-Mugabe ya rasu ne a kasar Singapore ranar 6 ga watan Satumba, 2019

Iyalan marigayi tsohon Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe na shirin bude gidan tarihi domin tunawa da mamacin a kauyensa na Zvimba inda aka binne gawarsa, a cewar wani rahoto.

Leo Mugabe wanda yake matsayin da a wurin marigayin ya ce wannan gidan tarihin zai yi matukar kyau sosai kasancewarsa a kauyen marigayin za yi shi.

KU KARANTA:NYSC ta kama mutum 95 da takardun makaranta na bogi

“Za mu mayar da wurin da aka binne gawarsa gidan tarihi ta yadda kabarinsa na tsakiya sai kuma daga gefe mutane za su iya kaiwa da komowa.

“Ko shakka babu hakan shi ne abu mafi da cewa, saboda na farkon da muka so budewa bai kai girman wannan din ba.” Inji Leo.

Leo Mugabe dai shi ne ke magana da yawon iyalan Mugaben kuma shi ne ya shaidawa ZTN wannan labari.

Idan baku manta ba, Mugabe ya rasu ne yana da shekaru 95 a duniya, ranar 6 ga watan Satumba a kasar Singapore bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

Ita dai gwamnatin kasar Zimbabwe a wurin daban ta so a binne gawar tsohon shugaban kasan, inda har ta soma gyara wurin binne gawar.

Daga bisani kuma iyalan marigayin suka canja shawara inda suka bukaci gwamnatin ta ba su gawar domin sun binne shi a kauyensu na Zvimba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel