Zamfara: Jami'an EFCC sun gano makuden kudade a ofishin INEC (Hotuna)

Zamfara: Jami'an EFCC sun gano makuden kudade a ofishin INEC (Hotuna)

Jami'an hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati EFCC, a ranar Laraba sun kai ziyarar bazata ofishin hukumar Zabe mai zaman kanta na kasa INEC, reshen jihar Zamfara inda suka gano jakunkunna cike da kudi.

Ana kyautata zaton kudin na cikn naira miliyan 84.6 da ya kamata a biya ma'aikatan wucin gadi ne da wasu shugabanni na hukumar suka karkatar yayin babban zaben 2019.

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa jami'an na EFCC sun dira ofishin INEC na Gusau a cikin mota kirar Toyota Hiace kuma suka fice dauke da jakkuna hudu makil da kudi. An ce sun kwato kudaden ne daga ofishin akantan hukumar.

DUBA WANNAN: Albashin shugabanni da 'yan majalisun dattijai da na wakilan tarayya

A baya jami'an na EFCC sun kama wasu ma'aikatan INEC hudu suka musu tambayoyi sannan daga bisani aka mayar da su ofishin na INEC da ke Gusau bayan an gama bincike a ofishin.

Majiyar ta ce, "Jami'an na EFCC sun kuma tafi da wasu takardu sun kuma tafi da wasu ma'aikata daga ofishin na INEC da ake zargi da hannu aikata ba dai-dai ba."

Kama ma'aikatan na INEC na zuwa ne bayan wani daga cikin ma'aikatan wucin gadi da ya yi aikin zaben 2019 ya shigar da korafi a ofishin.

Ma'aikacin ya yi ikirarin cewa ma'aikatan na INEC sun tauye musu wasu hakokinsu yayin biyan kudin aikin zaben.

Hukumar ta EFCC ta ce babu ma'aikacin wucin gadin da aka biya shi kudinsa baki daya kamar yadda aka biya takwarorinsu a wasu jihohi. An ruwaito cewa dukkan kudin ya kai naira miliyan 84.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel