Satar dalibai 6: Har yanzu muna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen - Kwamishanan yan sandan Kaduna

Satar dalibai 6: Har yanzu muna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen - Kwamishanan yan sandan Kaduna

- Kwanaki shida kenan da yin garkuwa da dalibai 6 da malamai 2 a makarantar Engravers College dake Kaduna

- Wannan ya biyo bayan garkuwa da daliban jami'ar ABU guda shida a makonnin bayan

- Hukumar yan sandan jihar tace ta san inda masu garkuwa da mutanen suke amma sun tsoron sanya rayukan yaran cikin hadari

Kwamishanan hukumar yan sandan jihar Kaduna a ranar Laraba ya bayyana cewa har yanzu ana tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da daliban makarantan sakandare 6 da malamai biyu a ranar 3 ga watan Oktoba.

Kwamishanan yan sanda, Ali Janga, ya kara da cewa hukumar ta damke masu garkuwa da mutane 50 a wurare daban-daban na sassan jihar kuma sun kwato bindigogi 27.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Kaduna inda ya ce an yanke shawarar sulhu da masu garkuwa da mutanen saboda gudun sanya rayukan daliban cikin hadari.

KU KARANTA: Majalisar dattawa na shirin kafa dokar shekaru 5 a gidan Yari ga malaman jami'a masu neman lalata da dalibansu

Yace: "Muna ciniki da masu garkuwa da mutanen domin ceto yaran da malamansu, mun san inda barayin yaran suke amma bamu son sanya rayukansu cikin hadari."

"Yawancin wadannan masu satar mutanen suna ta'amuni da muggan kwayoyi, saboda haka kisa ba komai bane a wajensu, wannan shine dalilin da yasa muke tattaunawa dasu kuma muddin an sakeso zamu fitittikesu."

"Muna tabbatarwa mutan jihar Kaduna cewa zamu kama masu garkuwa da mutanen nan ba da dadewa ba.

"Makarantar ta riga ta yi kuskure amma za muyi iyakan kokarinmu wahen ceto su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel