Yadda na kashe wata babbar kwamandar sojin ruwa – Mai laifi

Yadda na kashe wata babbar kwamandar sojin ruwa – Mai laifi

Yan makonni bayan kashe kwamandar makarantar sakandare na sojoji da ke Jaji, kwamanda Oluyemisi Ogundana, babban wanda ake zargi, Bernard Simon ya bayyana yadda ya kashe babbar sojar ruwan.

Simon wanda ya kasance cikin mutane 50 da kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, Ali Aji Janga ya gurfanar a ranar Laraba, yace shi kadai ya kashe kwamanda Ogundana.

CP Janga yayinda yake gurfanar da makashin yace, ya yiwa sojar fyade ne har lahira.

Sai dai kuma sabanin haka, Simon ya karyata yiwa kwamadar sojin fyade kafin ko bayan kashe ta.

Ya bayyana cewa sabanin ikirarin cewa, dashi da wani ne suka kashe sojar, shi kadai ne ya aikata hakan lokacin da ya saci hanya ya shiga gidanta a sansanin soji na Jaji sannan ya buga mata karfe a kai.

Yace ya kashe ta ne saboda tana cutarsu a makaranta. Yace shi malami ne a makarantar sannan cewa tana cutarsu a matsayinsu na ma’aikata dake karkashinta.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattijai ta fara tattauna wa a kan dokar hukunta lakcarorin da ke lalata dalibai

Yace ya kashe ta ne domin yanta ma’aikatan da take cuta.

Yace musamman shi akwai naira 100,000 da ta tauye masa shiyasa ya aikata hakan a kanta. Sai dai yace yayi danasanin abunda ya aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel