Majalisar dattawa na shirin kafa dokar shekaru 5 a gidan Yari ga malaman jami'a masu neman lalata da dalibansu

Majalisar dattawa na shirin kafa dokar shekaru 5 a gidan Yari ga malaman jami'a masu neman lalata da dalibansu

- Majalisar dattawa na kokarin dawo da dokar hukuncin shekaru biyar ga malaman jami'a malalata

- Za ku tuna cewa majalisar da ta shude ta yi kokarin kafa wannan doka amma basu cimma manufa ba

- Wasu sanatocin da suka ki dokar sunce bai kamata ace malaman jami'a kadai zai shafa ba

A ranar Laraba, 9 ga Oktova, majalisar dattawan Najerya ta yanke shawarar sake dauko dokar da Sanata Ovie Omo-Agege ya kawo a shekarun baya kan hukunta malaman jami'an da aka kama da laifin kokarin lalata da dalibansu.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa dokar ta bukaci hukuncin shekaru biyar a gidan maza da taran Milyan biyar ga duk malamin jami'ar da aka kama da laifin kokarin lalata da dalibi mace ko namiji.

Dokar ta ce duk malamin da aka kama da wannan laifi zai iya kwashe mafi akasari, shekaru biyar a gidan maza amma ba kasa da shekaru biyu ba.

Amma a lokacin an samu cikas yayinda shugaba Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu.

Dalilan da yasa wasu yan majalisan basu goyi bayan dokar ba a baya shine bai kamata ace dokar ta mayar da hankali kan malaman jami'a kadai ba, amma dukkan wanda aka kama da irin laifin.

Bayan rahoton BBC da ta bayyana wasu malaman jami'ar Legas da jami'ar Ghana, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo Agege ya sake dawo da dokar majalisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel