Majalisar dattijai ta fara tattauna wa a kan dokar hukunta lakcarorin da ke lalata dalibai

Majalisar dattijai ta fara tattauna wa a kan dokar hukunta lakcarorin da ke lalata dalibai

A ranar Laraba ne majalisar dattijai ta fara tattauna wa a kan bukatar yin dokar hukunta lakcarorin da ke tilasta dalibai yin lalata da su domin basu gurbin karatu ko kuma basu maki a jarrabawa.

Mamba a majalisar dattijai kuma mataimakin shugaban majalisar, Ovie Omo-Agege (dan jam'iyyar APC daga jihar Delta), shine wanda ya fara gabatar da kudirin a lokacin waccan majalisar, majalisa ta 8.

Kudirin, wanda aka fara gabatar da shi a watan Oktoba na shekarar 2016, ya nemi a daure duk wani lakcara da aka samu da laifin neman daliba da lalata na tsawon shekaru biyar a gidan yari.

A cewar kudirin, "hukuncin daurin shekaru 5 zai hau kan duk wani malamin makaranta da aka samu da laifin yin lalata da dalibar da shekarunta basu wuce shekaru 18 ba, ko kuma neman daliba da lalata domin samar mata gurbin karatu ko kuma bata maki a jarrabawa ko kuma nemar mata tallafin karatu ko wata kyauta."

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada wa mambobin kwamitin ECA a ganawarsu ta farko

Duk da majalisa ta 8 ta amince da wannan kudiri, kudirin bai zama doka ba saboda shugaban kasa bai saka hannu a kansa ba.

Wasu daga cikin mambobin majalisar dattijai sun nuna adawarsu da kudirin bisa hujjjar cewa dokar ta tsaya ne a iya kan malaman jami'o'i kawai.

Sanata Omo-Agege ya sake gabatar da kudirin a gaban majalisar a ranar Laraba bayan gidan jaridar BBC ya wallafa wani faifan bidiyo na wasu lakcarorin jami'ar Legas da aka yi amfani da na'urorin fasahar zamani wajen kama malaman yayin da suke neman daliban da lalata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel