'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 4 da suka musu kwantar bauna

'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 4 da suka musu kwantar bauna

'Yan sanda a jihar Edo sun kashe wasu mutane hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne yayin wata musayar wuta da suka yi.

The Punch ta ruwaito cewa majiya daga rundunar 'yan sandan ta ce masu garkuwa da mutanen suna hanyarsu ta zuwa sato wani babban mutum ne kwatsam sai suka hadu da 'yan sandan a kusa da Ogbaci River a wajen garin Benin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Danmallam Muhammed ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin a Benin inda ya ce ba don jami'ansa suna cikin shiri ba da an samu labari mara dadi bayan da suka afka tarkon masu garkuwa da mutanen.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

Ya ce, "Ba wai farautar masu garkuwa da mutanen aka tafi yi ba. Jami'an 'yan sandan sun fada cikin tarko ne amma jami'an namu suna cikin shiri kuma cikin gaggawa suka ankare suka kashe guda hudu cikin masu garkuwa da mutanen yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunin bindiga."

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wata tawagar jami'an tsaro na hadin gwiwa ta Rundunar 'yan sandan jihar Borno da jami'an Operation Puff Ader sun yi nasarar kama wasu manyan wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi 17 a jihar.

Yayin baje kolinsu ga masu manema labarau, 'yan sandan sun bayyana abubuwan da suka kwato daga mutanen da suka hada da; ganye da ake zargin wiwi ne, s*ck and die, kwayan Drazzapan da tukunyan shan Shisha.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Ndatsu ya ce, "Kana iya ganin abubuwan da muka kwato, busasun ganyayyaki da ake zargin wiwi ne, s*ck and die mai yawa, kwayar Drazzapan, tukunyar shan Shisha da ake amfani dashi wurin busar ganyayakin da ake badda kama da su kamar ganyen Shisha."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel