Kwastam sun samu N4.99b a cikin Watan Satumba a filin jirgin MMIA

Kwastam sun samu N4.99b a cikin Watan Satumba a filin jirgin MMIA

Dakarun hukumar Kwastam masu maganin fasa kaurin da ke aiki a babban filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas sun samu kusan Naira biliyan a cikin Watan Satumban jiya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust ta ranar 9 ga Watan Oktoban 2019, jami’an hukumar sun bayyana abin da su ka samu a Satumba a matsayin N4, 991, 674, 905.00.

Hukumar ta tatsowa gwamnatin kasar abin da ya nemi ya kai biliyan 5 ne a matsayin kudin shigo da kaya a iyakar filin jirgin. Wannan makudan kudi dai sun zarce abin hukumar ta sa ran samu.

A irin wannan lokaci shekarar bara ta 2018, hukumar kwastam ta samu N3, 976, 291, 655. 00 ne. Wannan kari na sama da Naira biliyan guda ya nuna cewa jami’an kasar sun yi namijin kokari.

KU KARANTA: An soma zama a kan kasafin kudin shekarar 2020 a Majalisa

Rahoton yace bayan adadin kudi da gwamnati ta samu wajen shigowa kasar, jami’an hukumar NCS sun kuma yi nasarar dakile wasu kaya da aka yi yunkurin shigo da su cikin kasar a sace.

Daga cikin kayan da aka karbe a filin jirgin a watan jiyan akwai jirage maras matuki wadanda ba su da takardun shaida, akwai kuma wayoyin salula, sai kuma wasu kayan sojoji da dai sauransu.

An cin ma wannan nasara ne bayan Misis Lena E. Oyama ta zama shugaban jami’an kwastam da ke aiki a filin jirgin. Lena E. Oyama tace sun dauki sababbin matakai da su ka hada da kara tsauri.

Kakakin hukumar, Ephraim Haruna, a wani jawabi ya ce Oyama ta kawo sabon tsari na ganawa da manyan Dakaru da kuma sauya ma’aikata. An kuma ragewa wasu kusoshi na hukumar karfi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel