Rigingimu: Mambobin PDP sun fice daga zauren majalisar dokokin jihar Filato

Rigingimu: Mambobin PDP sun fice daga zauren majalisar dokokin jihar Filato

An dakatar da zaman majalisar jihar Plateau na ranar Laraba cikin gaggawa domin kaucewa barkewar rikici tsakanin 'yan majalisar.

Rikici ya fara ne bayan kakakin majalisar ya karanto wata wasika da gwamnan jihar Simon Lalong ya aikewa majiyar na bukatar a amince masa ya nada sabon kwamiti da za su rika kulawa da kananan hukumomi hudu a jihar.

Nan take majalisar ta rabu kashi biyu inda 'yan jam'iyyar APC masu rinjaye suke goyon bayan amincewa da bukatar gwamnan yayin da mambobin jam'iyyar PDP marasa rinjaye suka ce ba za ta sabu ba.

The Nation ta ruwaito cewa 'yan majalisar na PDP sun ki amincewa da bukatar gwamnan ne domin ta sabawa sashi na 7, sakin layi na (1) da (2) na kudin tsarin mulkin 1999 da ya bayar da ikon zaban shugaban karamar hukuma ta hanyar yin zabe.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

Dukkan 'yan PDP sun ki amincewa da bukatar na gwamnan wadda suka ce ta sabawa doka kuma wani yunkuri ne na hana mazauna kauyuka zaban shugaban da suke kauna. Sun kuma ce wannan yi wa demokradiyya fyade ne.

Kakakin majalisar, Ayuba Abok da sauran 'yan APC sun tubure cewa dole sai an amince da bukatar da gwamna. Hakan ya sanya 'yan jam'iyyar PDP a majalisar suke fice waje domin yin zanga-zanga a harabar majalisar.

Shugaban marasa rinjaye Peter Gyendeng ya shaidawa manema labarai a harabar majalisar cewa abinda takwarorinsu suka aikata na bawa 'yan APC mukami ya sabawa doka kuma mulkin kama karya ne da neman hana mutane zaban wadanda za su wakilce su.

Duk da zanga-zangar da 'yan jam'iyyar na PDP su kayi, daga bisani Gwamna Lalong ya rantsar da kwamitin na masu kulawa da kananan hukumomin da dakin taro na Banquet a gidan gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel