Abinda Buhari ya fada yayin ganawarsa da tsofin ministocinsa

Abinda Buhari ya fada yayin ganawarsa da tsofin ministocinsa

A ranar Laraba, 9 ga watan Oktoba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wasu tsoffin ministoci da suka yi aiki tare dashi a lokacin da yake shugabain watan Janairun 1984 da Agusta 1985.

Shugaban kasar wanda ya gana da tsofin ministocin Abuja, ya tuna “yadda muka gudar da abubuwa a lokacin,” saboda ya kasance mulkin soja.

A yayin ganawar tasu, shugaba Buhari ya sha alwashin “tafiya tare da kowa a wannan mulki nawa na karshe a matsayin zababben Shugaban kasa na damokradiyya.”

Yayi godiya ga tsoffin ministocin “akan yawan tuntubarsa” da kuma yaba wa rundunar soji akan gida Abuja a matsayin babban birnin tarayyar kasar.

Jagoran tawagar, Farfesa Ibrahim Gambari, wanda ya rike mukamin ministan harkokin waje a waccan lokacin, ya ce sun ziyarci Buhari ne domin taya shi murna a kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin tsaro, harkokin kasashen waje, yaki da cin hanci, ilimi da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Ya farke laya: Tsohon jigon PDP a Jigawa ya bayyana dalilinsa na komawa APC

Yace: “An nada mu a shekaru 35 da watanni tara da suka gabata. Mu goma sha takwas aka rantsar.

"Shugabancinka ya kasance tabbatace, amma ka bamu dammar aiki kai tsaye. Ka san duk abunda kowa ke yi. Ba za mu taba mantawa da damar da ka bamu ba. Za mu cigaba da biyayya,” inji Gambari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel