Ya farke laya: Tsohon jigon PDP a Jigawa ya bayyana dalilinsa na komawa APC

Ya farke laya: Tsohon jigon PDP a Jigawa ya bayyana dalilinsa na komawa APC

Alhaji Rabiu Dangabi, tsohon jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a Jigawa, yace ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ne saboda kyakyawan aikin Gwamna Muhammad Badaru.

Ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Dutse a ranar Laraba, 9 ga watan Oktoba.

Dangabi, wanda ya kuma kasance tsohon dan majalisar dokokin jihar, yace bai koma jam’iyyar domin samn mukamin siyasa ba.

“Babu wani abu mai kama da yarjejeniya tsakanina da kowa cewa idan na koma APC, za a bani mukamin siyasa ko za a ba wani daga cikinmu mukami idan ya sauya sheka.

“Nayi mamakin dalilin da yasa mutane ke has ashen cewa mun zo ne domin anyi mana alkawarin za a bamu mukaman siyasa.

KU KARANTA KUMA: Karin harajin kaya: Za a yi amfani da kudaden a fannin lafiya, ilimi da gine-gine – Buhari

“Abunda mutane ke fadi ba gaskiya bane, mun yanke shawarar yasar da PDP ne saboda kyakyawan aikin Gwamna Muhammadu Badaru da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Mun yarda da manufofin APC wannan ne yasa muka bar jam’iyyarmu, PDP sannan muka koma APC,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel