Tashin hankali: Kauyuka muke bi ko zamu samu budurwar da zamu yiwa fyade tunda bamu da kudin da zamu nemi karuwai muyi zina da su - In ji Shafi'u Isah

Tashin hankali: Kauyuka muke bi ko zamu samu budurwar da zamu yiwa fyade tunda bamu da kudin da zamu nemi karuwai muyi zina da su - In ji Shafi'u Isah

- Wasu samari guda uku da aka kama a jihar Neja sun bayyana yadda suke yiwa mata fyade

- Samarin an kama su da laifin yiwa wata budurwa fyade a garin Paikoro dake cikin jihar ta Neja

- Sun bayyana cewa sun jima suna yiwa mata fyade ba a taba kama su ba sai a wannan karon, sun kuma kara da cewa gari-gari suke bi ko zasu samu wacce za su yiwa fyade tunda basu da kudin da zasu je su nemi karuwai

Wasu matasan samari da aka kama da laifin yiwa wata budurwa mai shekaru 20 fyade a Paikoro dake jihar Neja, bayan mahaifin budurwar ya kai su kara.

Matasan masu suna Shafiu Isah mai shekaru 19, Jawalu Babuga mai shekaru 19, sai kuma Musa Sabiu mai shekaru 18, sun kama budurwar ne a lokacin da ta dawo daga wajen aiki inda suka yi mata fyade.

Matasan sun bayyana cewa sun jima suna yiwa mata fyade kuma ba a taba kama su ba sai a wannan karon.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kashe wani kare da aka ganshi da kan jariri a Abuja

A cewar daya daga cikin su: "Muna zuwa Kauyuka Kauyuka muna neman macen da zamu yiwa fyade ne tunda bamu da kudin da zamu bawa mace muyi zina da ita."

Matsala akan fyade na kara tsamari duk kuwa da irin kokarin da hukumomin tsaro suke yi a kansu a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel