Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kashe wani kare da aka ganshi da kan jariri a Abuja

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kashe wani kare da aka ganshi da kan jariri a Abuja

- An yiwa wani katon kare ruwan itatuwa da duwatsu a barikin sojoji ta Mambila dake babban birnin tarayya Abuja

- An kashe karen ne bayan ya hau wani karamin yaro dan shekara daya da cizo, inda har yayi sanadiyyar kashe shi

- An bayyana cewa karen na wani babban soja ne a barikin, sai dai mutane sun dauki wannan matakin ne da niyyar ceto rayuwar yaron

An kashe wani katon kare bayan an kwace kan wani yaro jariri da aka ganshi a bakin shi a barikin sojoji na Mambila dake babban birnin tarayya Abuja.

An bayyana cewa karen na wani babban soja ne dake zaune a cikin barikin.

A yadda rahotanni suka bayyana, yaron yana zaune yana wasan shi sai karen ya ganshi, kawai sai yaje ya kama kanshi ya cire.

Bayan mutane sun ga abinda ya faru sai suka hadu suka dauko itatuwa da duwatsu suka fara dukan karen, amma maimakon ya saki kan yaron, sai yaki saki har sai da suka kashe shi har lahira aka samu aka cire kan yaron daga bakin shi.

KU KARANTA: Ta tabbata auren jaruma Sadiya Adam ya mutu, bayan an ganta ta koma otal da zama

Bayan an kwaci yaron da kyar aka wuce dashi asibiti, sai dai da zuwa asibitin yace ga garinku nan.

Wannan dai sabon abu ne a wajen mutane da yawa, domin kuwa ba kasafai aka fiya samun dabba tana cutar da yara kanana ba, sai dai akwai wanda suna tsoratar da yaran amma ba za su cutar da su har ta kai ga sun kashe ba baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel