Kotu ta yankewa wata budurwa shekaru 10 a gidan gyaran hali akan kisan kai

Kotu ta yankewa wata budurwa shekaru 10 a gidan gyaran hali akan kisan kai

- A ranar Laraba ne wata kotu da ke zama a jihar Legas ta yankewa wata budurwa mai suna Blessing Edet hukuncin shekaru 10 a gidan yari

- Kotun ta kama Blessing ne da laifin sukar saurayinta a ciki inda har ya rasa rayuwarsa

- Kotun ta yanke mata shekaru 10 ne a maimakon daurin rai da rai sakamakon ganowa da tayi cewa budurwar ta yi kisan ne wajen yunkurin kare kanta

A ranar Laraba ne wata kotu ta yankewa Blessing Edet mai shekaru 27 hukuncin shekaru 10 a gidan yari akan kashe saurayinta.

Blessing ta kashe saurayinta mai shekaru 33 ta hanyar soka masa wuka akan kin saka zobensa da ya bata.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, da farko an zargi Edet da laifin kisan kai. Amma kuma daga baya sai alkalin ya kara duban shari'ar inda aka gano kare kanta tayi wanda hakan ne ya kai ga kisan kai.

KU KARANTA: Wasu mabiya sun ja shugaba a kasa akan rashin cika alkawari

"A sokawa mamacin wuka da tayi, ba ta yi nufin raunata shi ba. Tabkuma bada dalilan da suka sa ta kare kanta. A don haka ba za a yanke mata hukuncin kisa da gangan ba," in ji alkalin

Ya kara da cewa, "Sashi na 227 na hukuncin laifukan jihar Legas ya yanke hukuncin daurin rai da rai ga wanda ya yi kisan kai da gangan. A wannan kuwa, akwai ganganci ga mamacin da wacce ake karar,"

"A don haka ne na yanke mata hukuncin shekaru 10 a gidan yari ba tare da tara ba. Zamanta zai fara ne daga watan Agusta, 2015 lokacin da aka tsareta," in ji mai shari'a Taiwo.

An zargi Edet ne da cewa, a ranar 18 ga watan Augusta, 2015 da wurin karfe 12:15 na asuba a gidanta da ke lamba 1, layin Falana, Ogombo, Lekki, Legas, mamacin ya zo ya bukace ta da ta girka masa abinci wanda tace bazata iya ba. Shigarsa madafi ke da wuya ya hango zoben da ya bata a wajen risho. Hakan ya fusata sa har ya kai ga fasa madubi ya soketa dashi. Ta dinga kuka tana neman dauki daga makwafta.

Daga baya ta dauki wuka inda ta sokesa a cikinsa. An tsareta tun a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel