Wannan kasafin kudin haraji da bashi ne kawai - Sanata Abaribe ya caccaki Buhari

Wannan kasafin kudin haraji da bashi ne kawai - Sanata Abaribe ya caccaki Buhari

Shugaban marasa rinjayen majalisar dattawa, Sanata Eyinayya Abaribe, ya bayyana cewa wannan kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabtatar ba zai haifar da 'da mai ido ba saboda ya dogara kan haraji da yawa.

Sanatan ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayinda aka kaddamar da tattaunawa kan kasafin kudin a zauren majalisan dattawa.

Mista Abaribe ta laburta cewa a ra'ayinsa, kudin biyan bashi ya fi kudin ayyukan jin dadi yawa.

Yace: "Ina son sanyawa jawabin da shugaban kasa ya gabatar suna cewa wannan ba wani abu bane illa kasafin kudin haraji."

"Wannan kasafin kudi ne da ya dogara kan haraji. An jingina shi kan karin kudin haraji VAT zuwa 7.5%. Kudin biyan bashi ya fi kudin yin ayyuka yaa. An sanya tirilyan 2 don aiki amma za'a biya bashin tiriliyan 2.4"

KU KARANTA: Wasu mabiya sun ja shugaba a kasa akan rashin cika alkawari

A ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, 2019 shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin Najeriya ta shekarar 2012 ga majalisar dokokin tarayya.

Legit.ng Hausa ta kawo muku labarai kai tsaye kan yadda taron ya gudana. Hakalizak yanzu muna kawo muku lissafin kiyasin da aka gina kasafin kudin kai da hotunan taron:

Danyen man da za'a rika haka a rana: Ganga milyan 2.18

Farashin kowani Ganga daya a : $57

Farashin Dala: N305 / $

Kudin shigan da ake sa ran samu a shekerar 2020:

Dagar arzikin Man fetur : 2.64 trillion

Arzikin Sabanin Mai (Haraji) : 1.81 trillion

Sauran hanyoyi ( sauransu) : 3.7 Trillion

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel