Abinda Buhari ya fada wa mambobin kwamitin ECA a ganawarsu ta farko

Abinda Buhari ya fada wa mambobin kwamitin ECA a ganawarsu ta farko

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da mambobin sabon kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki (ECA) da ya kafa a fadar gwamnatin tarayya, Villa, da ke birnin tarayya, Abuja.

Yayin ganawar ta su, shugaba Buhari ya jaddada kudirin gwamnatinsa na fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

Shugaba Buhari ya shaida wa mambobin kwamitin ECA cewa tattalin arzikin Najeriya ba ya bunkasa kamar yadda ya kamata tare da sanar da su cewa yana bukatar su yi amfani da gogewarsu da iliminsu wajen zakulo hanyoyin da za a inganta tattalin arzikin Najeriya a cikin gida.

"Ina son yi muku godiya bisa amincewarku domin hidimtawa kasa. Akwai aiki mai muhimmanci a gabanku. Burin mu shine tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a cikin shekaru 10.

"Tabbas mun fita daga matsin tattalin arziki, amma har yanzu tattalin arzikin mu ba ya bunkasa ta yadda za mu samu sukunin cimma muradun mu

"A cikin gida ya kamata mu nemo hanyoyin inganta tattalin arzikin mu, ta yadda zai dace da tsarin kasar mu. Dole mu samar da wasu hanyoyi a cikin gida da zasu bunkasa tattalin arzikin mu. Ina jira da sauraron shawarwarinku a kan yadda za mu iya cimma hakan.

"Dukkan ma'aikatan gwamnati masu nasaba da aikin ku zasu iya gana wa da ku domin tattauna wa a kan yadda za ku iya taimaka musu," a cewar shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Sulaiman Adamu: Ministan Buhari ya ce jiharsa ta fi kowacce jiha kazanta a arewa

A ranar Litinin, 16 ga Satumba, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wasu mutane takwas a matsayin mambobin majalisar masu bashi shawara kan harkan tattalin arziki.

Wadanda Buhari ya nada sune:

1.Farfesa Doyin Salami – Shugaba

2. Dr. Mohammed Sagagi – mataimakin shugaba

3. Farfesa . Ode Ojowu – Mamba

4. Dr. Shehu Yahaya – Mamba

5. Dr. Iyabo Masha – Mamba

6. Farfesa Chukwuma Soludo – Mamba

7. Mr. Bismark Rewane – Mamba

8. Dr. Mohammed Adaya Salisu – Sakatare

Za su rika ganawa da juna sau daya a kowanne wata tare da ganawa da shugaban kasa sau hudu a shekara. Amma shugaban kwamitin zai iya ganawa da shugaba Buhari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel