Tsananin yunwa ta sanya 'yan ta'addan Boko Haram mika kansu ga rundunar sojin Najeriya

Tsananin yunwa ta sanya 'yan ta'addan Boko Haram mika kansu ga rundunar sojin Najeriya

- A ranar Laraba, rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan ta'addan Boko Haram 5 na bangaren Al-Barnawi sun mika kansu ga jami'an tsaro

- Shugaban yada labarai na rundunar, Col Aminu Iliyasu ya sanar da manema labarai cewa tsananin yunwa ce tasa 'yan ta'addan fitowa daga maboyarsu

- Rundunar sojin na cigaba da samun nasarori da yawa sakamakon tsananta takura ga 'yan ta'addan

Rundunar sojin Najeriya a ranar Laraba, ta ce 'yan ta'addan Boko Haram 5 na bangaren Al-Barnawi ne suka mika kansu ga rundunar bataliya ta uku sakamakon ragargaza maboyarsu da aka yi a arewa maso gabas.

Shugaban yada labarai na rundunar, Col Aminu Iliyasu, a takardar da ya bayyana ga manema labarai, ya bada sunayen 'yan ta'addan da suka mika kansu ga sojin. Sun hada da, Ramat Mohammed, Alhaji Brazil, Bukar Gambo, Waziri Bukar da Bashuna Musa.

KU KARANTA: Me yayi zafi? Dan sanda ya kashe budurwarsa daga baya ya kashe kansa

Kamar yadda takardar ta sanar, dole ta sanya 'yan ta'addan fitowa daga maboyarsu sakamakon yunwa da kuma bama-bamai da aka dinga sanyawa maboyar tasu.

Iliyasu ya bayyana cewa, rundunonin da ke aiki a yankuna daban-daban sun samu cigaba da dama sakamakon kara tsananta aikinsu da suka yi a fadin kasar nan.

Takardar ta ce, "A tsakanin 1 zuwa 8 ga watan Oktoba, 2019, rundunonin sojin Najeriya da ke aiki a fadin kasar nan sun samu cigaba mai yawan gaske. A tsakanin lokacin, sojin sun hana 'yan ta'addan rawar gaban hantsi wanda hakan ne ya kawo zaman lafiya ga mutane."

"A yankin arewa maso gabas, rundunar Operation Lafiya Dole, sun tsananta saka bama-bamai a maboyar 'yan ta'addan domin hana su tserewa. 'Yan ta'addan da yawa sun mika kansu ga rundunonin sojin," takardar ta kara da cewa.

"An kara takurasu ne da yunwa ta hanyar datse musu hanyoyin samun abincin." in ji takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel