Zargin tafka magudi: Gwamna Fintiri ya mayarwa Sanata Abbo martani

Zargin tafka magudi: Gwamna Fintiri ya mayarwa Sanata Abbo martani

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya yi kira ga Sanata Ishaku Abbo mai wakiltan mazabar Adamawa ya rika gabatar da kokensa ta hanyoyin da suka dace a maimakon yin zage-zage kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke mayar da martani kan zancen da sanatan ya yi cikin wani faifan bidiyo inda ya zarge shi da yin babakere da kuma tafka magudi a zaben cikin gida na kananan hukumomi na jam'iyyar PDP don kawar da wadanda ya ke ganin makiyansa ne.

Sanatan ya ce, "Ba zai yi wu mu nade hannu muna kalo a lalata mana jiha ba. Ni sanata ne, idan yana son ya yi fada da sanata ne, Allah ya bashi sa'a. A shirye na ke. Jam'iyyar PDP a jihar Adamawa tana fama da rashin lafiya, PDP a Adamawa tana dakin kulawa da masu rashin lafiya an kuma sa mata iskar Oxygen. PDP ta mutu."

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

A martanin gwamnan da ya yi ta bakin Direktan yada labaransa, Solomon Kumanga, ya ce bai dace a matsayinsa na sanata ya yi irin wannan ikirarin ba kuma ya shawarce shi ya bi hanyar da ta dace ya shigar da kararsa a maimakon zaginsa da ofishinsa.

Ya ce, "Mai girma gwamna ya yi takaicin abinda sanatan ya aikata kuma ya yi watsi da zage-zagen da cin mutuncin da aka yi wa ofishinsa. A halin yanzu gwamnan baya da niyyar yin rikic da sanatan.

"A maimakon haka, mai girma gwamna ya mayar da hankalinsa ne wurin kafa turbar ayyukan samar da tsaro, cigaba da inganta rayuwan al'umma da hukumomin jihar Adamawa kuma baya bukatar a rika dauke masa hankali."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel