Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta soma muhawara a kan kasafin kudin 2020

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta soma muhawara a kan kasafin kudin 2020

Majalisar dattawa ta soma gudanar da muhawara a kan kasafin kudin shekarar 2020 a yau din nan Laraba 9 ga watan Oktoba, 2019.

Idan baku manta ba, a jiya Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin na tiriliyan N10.33 a matsayin kasafin kudin shekarar 2020 a gaban gamayyar majalisar dattawa da ta wakilai.

KU KARANTA:Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: ‘Yan bindiga sun kashe jama’a da dama tare da satar shanu a wani kauyen Sakkwato

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi ya gabatar da wani lissafi na daban inda ya bukaci sauyi a wadansu bangaroran kasafin.

Har ila yau, Majalisar wakilai a nata bangaren ta fara gudanar da muhawara game da kasafin kudin shekarar 2020 domin yin bita a kansa gaba daya.

Wannan kasafin kudin na tiriliyan N10.33 shi ne kasafin kudi mafi yawo da aka taba gabatarwa a tarihin Najeriya. Kasasin kudin kamar yadda aka gabatar da shin a nuna cewa kasha ¼ (wato N2.345trn) na kudin za ayi amfani da shi ne wurin biyan bashi, yayin da naira tiriliyan 2.14 za ayi amfani da su domin gudanar da manyan ayyuka.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu, duk da cewa Shugaba Buhari ya fede biri har wutsiya game da kasafin kudin. Kingsley Chinda (PDP, Rivers) ya ce akwai bukatar a samu cikakken bayani game yadda aka tsara kasafin kudin ga ko wane sashe kafin majalisa ta amince da shi.

Haka zalika, a lokacin da Shugaban kasa ya ke gabatar da kasafin kudin ranar Talata, ya fadi cewa Zainab Ahmed ministar kudi za ta kawo cikakken bayanin kasafin kudin ga majalisar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel