Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da kwamitin basa shawara kan tattalin arziki (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya gana da kwamitin basa shawara kan tattalin arziki (Hotuna)

A ranar Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da mambobin kwamitin basa shawara kan tattalin arzikin Najeriya a fadar shugaban kasa, Aso Villa, birnin tarayya Abuja.

Mutane a fadin tarayya sun yabawa wannan kwamiti da Buhari ya nada saboda ingancin irin wadanda ya nada.

A ranar Litinin, 16 ga Satumba, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wasu mutane takwas cikin majalisar masu bashi shawara kan harkan tattalin arziki.

Wadanda Buhari ya nada sune:

1.Farfesa Doyin Salami – Shugaban

2. Dr. Mohammed Sagagi – mataimakin shugaba

3. Farfesa . Ode Ojowu – Mamba

4. Dr. Shehu Yahaya – Mamba

5. Dr. Iyabo Masha – Mamba

6. Farfesa Chukwuma Soludo – Mamba

7. Mr. Bismark Rewane – Mamba

8. Dr. Mohammed Adaya Salisu – Sakatare

Za su rika ganawa da juna sau daya wata tare da ganawa da shugaban kasa sau hudu a shekara. Amma shugaban kwamitin zai iya ganawa da shugaba Buhari a duk lokacin da ya bukata.

KU KARANTA: Kasar Italiya ta rage yawan yan majalisa daga 945 zuwa 600

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel