Wata sabuwa: Kungiyar kwadago tace bata aminta da N30,000 ba a matsayin sabon karancin albashi

Wata sabuwa: Kungiyar kwadago tace bata aminta da N30,000 ba a matsayin sabon karancin albashi

- A ranar Litinin da ta gabata ne kungiyar kwadago reshen jihar Legas ta ce bata aminta da N30,000 a matsayin karancin albashi ba

- Kungiyar ta sanar da hakan ne ta bakin shugabar kungiyar yayin da suke bikin murnar ranar halastattun aiyuka ta duniya wanda ake yi 7 ga watan Oktoba na kowacce shekara

- Shugabar ta ce, Legas jiha ce ta musamman gani da cewa sufuri da kudin haya ba daya yake da sauran jihohi ba

A ranar Litinin da ta gabata ne, ma'akatan gwanati a jihar Legas, sun ce ba zasu karbi kasa da N50,000 ba a matsayin karancin albashi.

Kamar yadda shugaban kungiyar kwadago na jihar, Funmi Sessi ta sanar, ta ce suna bukatar sake sabon ciniki gani da 'yadda Legas take'.

Ta jaddada cewa, ma'aikatan jihar Legas na fuskantar wahalhalu da yawa kafin su kai wajen aiki, don haka bazasu aminta da N30,000 ba a matsayin karancin albashin.

KU KARANTA: Hotunan bikin wata kyakyawar gurguwa da angonta sun jawo cece-kuce a arewa

Sessi tace, ba a biyan ma'aikatan yadda ya dace, wanda hakan ne ke kawo karin tabarbarewar lamurra.

Ta kara da cewa, sabuwar bukatar ma'aikatan ta biyo bayan bukatarsu ne yayin bikin ranar halastattun aiyuka na duniya, wanda ake yi duk ranar 7 ga watan Oktoba a fadin duniya.

Ta ce: "Dalili shine, Legas gari ne na musamman. Sufuri da kudin haya da hadurran da ke kan tituna ba daya yake da sauran garuruwa ba. Zuwa aiki ko kasuwa a nan, ba daya yake da jihar Ogun ba,"

"Bukatar mu itace, bayan an biya karancin albashi a N50,000 kuma muna so akalla a biya karamin ma'aikaci N15,000 alawus din hadurra." in ji ta.

Ta ce, "Lokacin da 'yan majalisar dattawa da na wakilai ke amsar miliyoyi, kunji wani labari? Amma biyan N30,000 a matsayin karancin albashi ya dau shekaru 2 ana ciniki."

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ma'aikatan sun yi tattaki a manyan titunan Legasa zuwa sakateriyar Alausa.

Ma'aikatan sun taru a gaban majalisar jihar Legas bayan tattakin lumanar da suka yi daga Ikeja kasan gada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel