Me yayi zafi? Dan sanda ya kashe budurwarsa daga baya ya kashe kansa

Me yayi zafi? Dan sanda ya kashe budurwarsa daga baya ya kashe kansa

- Wani dan sanda a kasar Afirka ta kudu ya hallaka budurwarsa har lahira inda daga baya ya kashe kansa

- Mai magana da yawun 'yan sandan yankin da abin ya faru, Tselanyane, ya tabbatarwa da manema labarai aukuwar lamarin

- An samu budurwar mai shekaru 27 da harbin bindiga a kanta inda shima saurayin yake kwance cikin jini

Wata budurwa mai shekaru 27 mai suna DJ Khanyi Ntanga an sameta a mace bayan da saurayinta Rustenburg mai shekaru 37 ya kasheta tare da kashe kansa.

Rustenburg jami'in dan sanda ne.

Jami'an 'yan sandan arewa maso gamma sun ce, an ga gawar masoyan ne a gidansu da kuma alamun dan sandan ya kashe kansa bayan yayi kisar.

KU KARANTA: Hotunan bikin wata kyakywar gurguwa da angonta ya jawo cece-kuce a arewa

Ana zargin dan sandan ya kashe kyakyawar budurwarsa ne inda daga baya ya dauki rayuwar kansa.

Mai magana da yawun 'yan sandan, Kaftin Sam Tselanyane ya tabbatarwa da manema labarai aukuwar lamarin a ranar 8 ga watan Oktoba. Ya ce, an kirasu ne wajen da aka yi harbin a Boitekong.

Kamar yadda Tselanyane ya sanar, an samu Ntanga ne da harbin bindiga a jikinta tare da saurayinta. 'Yan sandan sun ce sun fara bincike akan lamarin.

"Akwai raunin alburushi a kansa kuma yana kwance male-male cikin jini," in ji Tselanyane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel