Na so Ronaldo ya ci gaba da zama a Real Madrid - Messi

Na so Ronaldo ya ci gaba da zama a Real Madrid - Messi

- Lionel Messi ya yi ikirarin cewa bai ji dadin barin kungiyar Real Madrid da Ronaldo ya yi ba

- Dan wasan na Barcelona da Ronaldo sun shafe tsawon shekara goma suna kara wa juna kwazo

- Messi ya ce bai damu da cin kambun gwarzon dan kwallon kafa na shekara ba a karo na shida

Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya ce ya so babban abokin hamayyarsa a kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya ci gaba da zama a kungiyar Real Madrid ba tare da koma wa kungiyar Juventus ba.

'Yan wasan biyu sun kasance madubin duba wa musamman a wasan da ya fi shahara na gasar La Liga a kasar Andalus wanda ake yi wa lakabi da El-Clasico a tsawon shekaru goma da suka gabata.

Ana iya tuna cewa a shekarar 2018 ne dan wasa Ronaldo, ya sauya sheka inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke buga gasar Serie A a kasar Italiya bayan barin kungiyar Real Madrid.

Ronaldo dai ya bar Real Madrid a karshen kakar 2017/2018 bayan da ya lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere.

KARANTA KUMA: Justice Yahaya Jinaidu ya riga mu gidan gaskiya

A yayin da 'yan wasan biyu suka ci gaba da kasance wa masu haskaka kwallon kafa sanadiyar rashin disashewar tauraruwarsu tsawon fiye da shekaru goma, Messi ya ce tun bayan ficewar Ronaldo daga kungiyar Real Madrid, gasar La Liga sam da rage armashi.

Messi ya ce ya zuwa yanzu yana ci gaba da rashin jin dadin hukuncin da Ronaldo ya yanke na barin kungiyar Real Madrid, lamarin da ya ce arangamarsu a koda wane lokaci tana kara wa tamaula armashi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel