Justice Yahaya Jinaidu ya riga mu gidan gaskiya

Justice Yahaya Jinaidu ya riga mu gidan gaskiya

Da ya ke dai 'dan Hausa na cewa mutuwa rigar kowa kuma muddin ajali ya yi kira sai an amsa, mun samu rahoton cewa, Allah ya yi wa Justice Yahaya Abiodun Junaidu rasuwa bayan ya shafe shekaru 93 a doron kasa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, tarihi ya tabbatar da cewa, Justice Junaidu ya halarci makarantar sakandiren Methodist Boys High School ta jihar Legas, inda kuma ya zama cikakken lauya a shekarar 1954.

Ya kasance babban lauyan ma'aikatar shari'a ta Najeriya gabanin zama Alkalin babbar kotun jihar Legas a shekarar 1973.

Ya shahara da akidar tsayuwa bisa gaskiya tare da tabbatar da 'yancin hukumar shari'a ta Najeriya a matsayin mai cin gashin kanta. Ya yi ritaya daga Alkalanci a shekarar 1984.

Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe 2.00 na rana 10 ga watan Oktoban 2019 bisa tsari da karantarwa ta addinin Islama. Za'a kuma a binne shi a makabartar Vaults and Gardens da garin Ikoyin Legas.

KARANTA KUMA: Za'a biya mutumin da nono ya fitowa diyyar naira tiriliyan biyu

Ya tafi ya bar 'ya'ya ciki har da Mrs Olugbolahan Babalakin, mai dakin fitaccen lauyan nan kuma hamshakin dan kasuwa, Bolanle Olawale Babalakin.

Ana iya tuna cewa, a ranar Asabar 13 ga watan Afrilun 2019 ne tsohon ministan shari'a na Arewacin Najeriya a zamanin Sardauna kuma Galadiman Katsina, Justice Mamman Nasir ya riga mu gidan gaskiya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel