Gwamna AbdulRazaq ya sake aike wa da sunayen wasu kwamishinoni 6 majalisar dokokin jihar Kwara

Gwamna AbdulRazaq ya sake aike wa da sunayen wasu kwamishinoni 6 majalisar dokokin jihar Kwara

A karo na biyu, gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, ya sake aike wa da sunayen wasu zababbun kwamishinoni 6 zuwa majalisar dokokin jiharsa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, zababbun kwamishinonin da gwamna Abdulrazaq ya aike da sunayensu sun kasance hazikai a kan sana'o'in su kuma kwararrun shugabanni da suka yi fice a harkokin siyasa.

Makonni kadan da suka gabata ne gwamna Abdulrazaq ya gabatar da sunayen mata hudu a matsayin zababbun kwamishinonin jihar da suka hadar da wata mai shekaru 26, Joanna Kolo.

Sabbin zababbun kwamishinonin shida da gwamna Abdulrazaq ya sake aike wa majalisar dokokin sunayensu tare da yankunan da suka fito sun hadar da; Salman Jawondo (Asa); Lafia Aliyu Kora Sabi (Baruten); Dr. Raji Razaq (Ekiti); Architect Aliyu Mohammed Saifudeen (Kaiama); Wahab Agbaje (Whyte, Offa); da kuma Murtala Olarewaju (Oyun).

KARANTA KUMA: Mutune 4 sun dulmiye a ruwa wajen daukar hoto na 'selfie a Indiya

Kakakin majalisar dokokin jihar, Yakubu Salihu, shi ne ya bayar da shaidar isowar wasikar gwamnan a ranar Laraba.

Bayan karance wasikar gwamnan tsaf, Honorabul Salihu ya ce majalisar za ta yi iyaka bakin kokarinta wajen tabbatar da macancanta sun karbi akalar jagoranci a jihar, tare da cewa nan ba da jima wa ba za'a bayyana lokacin tantance zababbun kwamishinonin.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel